Jajibirin jefa kuri'ar jin ra'ayi akan ko 'yan kasar Girka zasu yi na'am da ka'idodin da aka gitta ma kasar na bata ranchen ceton tattalin arzikin kasar, Ministan kudi na kasar Girka ya zargi masu baiwa kasar sa bashi da laifin ta'adanci.
Ministan ya fadawa wata jaridar harshen Spanish mai suna El Mundo cewa abinda masu baiwa kasar sa bashi suke yi yana da suna, sunan sa ta'adanci. Yace abinda kasashen turai suke so, shine yan kasar Girka su jefa kuri'ar yin na,am da sharuddan aka gitta wa kasar, domin su samu nasarar cin mutuncin ya kasar Girka.
Yau Asabar jaridar ta wallafa wannan hira jajibirin jefa kuri'ar jin ra'ayi akan ka'idodin da kasashe turai suka gitta wa kasar na bata bashin ceton tattalin arzikin kasar.
Prime Ministan Girka yayi kira ga masu jefa kuri'a da su jefa kuri'ar rashin amincewa.
Prime Ministan ya fada a jiya Juma'a cewa jefa kuri'ar rashin amincewa zai baiwa yan kasar Girka damar gudanar da rayuwa cikin mutunci a turai kuma zai baiwa gwamnatin kasar karin karfin gwiwar yin shawarwari da masu bata bashi.
Ministan kudin na kasar Girka, yace masu baiwa kasar sa bashi, suna son yan kasar suyi na'am da sharuudan da aka gittawa kasar, domin su samu zarafin wulakanta kasar Girka