Buhari ya bayyana haka ne a ga ‘yan Najeriya a kasar Kenya da ya kai ziyara. Ya fadi cewa, karya Naira ba abinda zai ja wa talakan Najeriya sai karin azabar rayuwar da a yanzu suke fuskanta sakamakon nakasashshen tsarin tattalin arziki da aka bi a baya.
Ya kara da cewa, gwamantocin baya sun bi rarraunar hanyar da bata dace da rauywawar talakawa ba ta yadda za su amfana daga dimbin arzikin da Allah ya yiwa giwar nahiyar Afirka din. Shugaban ya ce in har zai yarda da karya darajar Naira, to kuwa masana tattalin arziki na da jan aikin samun amincewarsa.
Inda yake bayyana musu cewa sai an yi masa bayanin gamsashshe kuma mai cike da hujjojin yin hakan. Wani masanin tattalin arziki Malam Sani Aminu Dutsin-Ma, ya bayyanawa Wakilinmu Umar Faruk Musa cewa, wannan shawara ta Buhari abar dubawa ce.