Washington, DC —
Shirin Baki Mai Yanka wuya a wannan makon ya yi nazrin babban zaben kasar Ghana na shekarar nan ta 2024 da aka kammala, da kuma darussa da ababen koyi da dama da za a iya koya daga zaben.
Duk da yake dai ba a rasa ‘yan matsaloli ba nan zuwa can, zaben, ya sami karbuwa, yabo da jinjina a idon duniya, inda hukumomi, manazarta, masu sa ido, har ma da daidaikun jama’a suke bayyana cewa kasar ta Ghana, tana aikewa ne da babban darasi ga sauran kasashe masu da’awar bin tsarin dimokaradiyya, musamman a nahiyar Afirka.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna