Gawar tsohon gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ta iso Najeriya daga kasar Jamus don shirin yi mata jana’iza.
An iso da gawar ne ta filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas inda matarsa Betty Anyawu Akeredolu da ke cikin tawaga ta tarbi gawar tana mai zubar da hawaye.
Kazalika ‘ya’yansa da ‘yan uwansa ciki har da kaninsa da ke binsa Farfesa Wole Akeredolu na wajen tarbar gawar.
Gwamnonin Legas, Osun da Ogun sun turo wakilansu wajen tarbar gawar.
Akeredolu ya yi fama da cutar daji na tsawon watanni da hakan ya sanya shi kwantawa a asibitin Jamus inda rai ya yi halinsa yana mai shekaru 67.
Gabanin rasuwar tasa, Akeredolu ya yi jinyar farko a kasar ta Jamus, inda daga baya ya dawo bayan kwshe watanni.
Sai dai ya yada zango a birnin Ibadan a lokacin da ya dawo inda daga nan aka sake mayar da shi asibitin na Jamus.
In za a tuna, tuni aka rantsar da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa wanda ya tsallake rijiya da baya wajen tsigewa ya zama sabon gwamnan jihar ta Ondo.
Dandalin Mu Tattauna