Gasar mawaka ta Freedom Radio, wato 'Freedom Radio Meko Award' a karo na biyu ta samu hallartar mawaka kimanin 72 da suka samu damar shiga gasar, inda mawaka 16 suka samu zuwa matakin karshe.
A cikin su 16, mawaka hudu na bangaren nanaye da fadakarwa ne, sannann mawaka hudu kuma na bangaren nishadantarwa zalla, yayin da bangaren gambarar zamani wato Hip-hop aka samu mawaka guda hudu, sannan hudu a bangaren nishadantarwa zalla.
A duk cikin wannan bangaren na wadanda suka zo mataki na karshe, mawakiya daya ce mace, wacce ta cire tuta wajen fafatawa da mawaka maza, nasarar da ta kwatantata da zama zakarar gwajin dafi, sunan mawakiyar Queen Zeeshaq.
Daya daga cikin fitattun mawakan Hausa da ya hallarci taron don sanya ido, wato mawaki Ado Isa Gwanja, ya ce yana da kyau kafafen yada labarai su dinga shirya makamanciyar wannan gasar, don karfafawa mawaka gwiwa wajen inganta wakokinsu.
Shima wani jigo a bangaren Hip-hop Bello Ibrahim wanda aka fi sani da Billy-O, ya ce ya kamata gwamnatoci da malamai su shigo cikin harkar mawaka domin tsaftace masana’antar.
Mai gayya mai jama'a shugaban kwamitin shirya gasar Freedom Meko Award, Nura Bello wanda aka fi sani da 'Belnur' ya ce ya ji dadin yadda mawaka da dama suka bada hadin kai wajen tabbatar da wannan gasa.
Gasar dai zata dauki nan da mako guda kafin a bayyana waddan da suka yi nasara.
Facebook Forum