Ma'aikatan agaji a jihar pennsylvania sun tsunduma cikin mamaki a lokacin da suka dauko wani mara lafiya daga wani gida zuwa inda suka suka ajiye motarsu ta daukar marasa lafiya, amma da suka fito ba su ga motar ba.
'Yansanda a garin York ne suka gaya wa jami'an cewa, wani matashi dan shekaru 21 da haihuwa, mai suna Leonard Eugene Smith ne ya dauki motar da niyyar ya dana kafin ya je ya ajiye ta wani wuri. 'Yansandan suka kuma ce wata na'urar daukar hoto da aka kafe a cikin wata mota ce ta nuna abin da ya wakana sai kuma suka yi amfani da wata na'ura mai gano abubuwa don gano inda motar ta ke.
Mr. Jim Arvin, shugaban kamfanin motocin daukar marasa lafiya na White Rose Ambulance, ya fadi cewa hoton bidiyon ya nuna yadda Smith ya zazzaga a cikin motar kuma ga dukan alamu ya ji dadin abinda yayi.
An tuhumi smith da aikata babban laifi, sata, da kuma yin barazana ga rayukan jama'a bisa ganganci. Yanzu haka dai an garkame shi kuma sai da dala dubu saba'in da biyar za a iya yin belinsa.
Ba tare da bata lokaci ba aka kai maras lafiyan, mai fama da matsalar numfashi asibiti bayan da aka kira wata motar.