Shugabannin kasashen yankin Asiya da kuma sauran kasashen duniya sun bayyana kyakkyawar fata dangane da ganawar ta tarihi da aka yi yau Talata tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a Singapore.
Ganawar Shugaba Donald Trump Da Kim Joung Un
Shugaban Amurka Donald Trump yace takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un yanzu yana da damar inganta rayuwar al’ummarsa, ya kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Koriya.