Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitattun Malaman Addinin Islama Daga Najeriya Sun Ja Hankalin 'Yan Afrika Mazauna Turai


Sheikh Aminu Daurawa da Farfesa Mansur Isah Yelwa
Sheikh Aminu Daurawa da Farfesa Mansur Isah Yelwa

Wasu fitattun malaman addinin Islama daga Najeriya sun yi kira ga 'yan Afrika mazauna Turai da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin sauraran wa’azi daga bakin maluman a taron da aka saba gudanarwa shekara-shekara a Turai a kan muhimmancin zamantakewa mai kyau.

Sheikh Aminu Daurawa ne ya jagoranci taron da aka soma a Jamus da zummar ganin ya taimaka wajen kawo sauyi mai kyau da ci gaba a wajen mu’amala da zamantakewa ta fannin addini a tsakanin 'yan Afrika da ke zaune a nahiyar.

A karshen makon da ya shige ne Kungiyar Afrika ta Ummah a Turai reshen Jamus ta bude taron, inda aka ja hankalin mahalarta a kan muhimman al’amura da suka shafi rayuwa ta iyali da zamantakewa tsakanin juna.

Taron al’umar Musulman Afirka a yi a Jamus
Taron al’umar Musulman Afirka a yi a Jamus

Daruruwan musulmi daga sassan kasashen Turai ne suka halarci taron, da daman suke cike da shaukin yin tozali da fitattun malaman addinin Islama na Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Farfesa Mansur Isah Yelwa na Jami‘ar Bayero a Kano, da kuma Limamin malami Abubakar Tafawa Balewa da ga jihar Bauchi a Najeriya.

Malaman da su ka fito daga Najeriya sun sami kyakkyawar tarba ta musamman daga sauran malumai da al’ummar musulmi da suka fito daga kasashen Afrika dabam dabam.

Taron al’umar Musulman Afirka a yi a Jamus
Taron al’umar Musulman Afirka a yi a Jamus

An dai yi Magana a kan daya daga cikin manyan matsalolin da al’ummar Afrika musamman Musulmai suka jima suna fuskanta a Turai, wadda ita ce ta rashin jituwa a tsakanin ma’aurata, abin da ya kasance daya daga cikin makasudin taron na bana.

Taron na tsawon kwanaki uku, an bude shi ne a birnin Oberhausen na kasar Jamus, inda za a ci gaba da gudanar da shi a birnin Hamburg a kuma karkare shi a kasar Belgium da ke makwabtaka da Jamus.

Fitattun Malaman Addinin Islama Daga Najeriya Sun Ja Hankalin Yan Afrika Mazauna Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG