Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’umomin Jihar Gombe Sun Mika Tallafi Ga Wadanda Masifa Ta Afkawa a Jihar Bauchi


Al’umomin jihar Gombe sun kai ziyarar jaje tare da tallafi ga mtuanen da ifti’la’in ruwa da iska da kuma gobara ta shafa a jihar Bauchi.

Da yake mikawa mataimakin gwamnan jihar Bauchi Alhaji Sule Abdu, gwamnan Gombe ya ce ya kai ziyarar ne domin jajantawa al’ummar Bauchi saboda halin da suka tsinci kansu ciki.

Al’umar Gombe dai ta mika tallafin Tirelar Shinkafa da Tirelar Masara, tare da kudi har Naira Miliyan 10.

Da yake jawabin godiya a madadin gwamnnatin jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Sule, ya bayyana farin ciki kan wannan ziyara da aka kai musu. Ya kuma bayar da tabbatacin cewa dukkan taimakon da aka bayar zai kai ga wadanda aka bayar dominsu.

Daga bisani gwamnnan jihar Gomben ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Bauchi, inda ya bayyana masa dalilinsu na zuwa Bauchi.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG