Yayinda wakilin Muryar Amurka ya ziyarci ofishin hukumar alhazai na jihar Legas ya ga maniyatta suna karban jakkunansu da sauran kayan guzuri irinsu garin kwaki da tabarmi da riguna da kuma samun bayanai.
Maniyattan da suka zanta da Muryar Amurka sun yaba da irin tanadin da gwamnatin Legas ta yi masu. Wani yace an taimaka masu matuka lamarin da ya sa komi ya zo masu da sauki.An basu abubuwa da dama da da can ba'a basu. Misali gwamnati ta basu abinci da riguna da ragunan layya duk da cewa gwamnan ba musulmi ba ne.
Wata ma tace shirin na bana nada kyau kodayake akan dauki lokaci. Shirin bana ya fi na baya kyau.
Maniyattan na bukatan wadanda zasu fadakar dasu akan aikin ibada a kasa mai tsarki. Suna fatan za'a taimaka masu ta yadda ba zasu sha wuya ba.
Tun farko gwamnan jihar ya kira maniyattan da su zama jakadu na kwarai tare da gudanar da addu'o'in samun zaman lafiya a kasar.
Ranar 23 na wannan watan za'a fara jigilar maniyattan daga Najeriya.
Najeriya gaba daya nada maniyatta fiye da 66,000.
Ga rahoton Babangida Jibrin