Bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato (FBI a takaice) ta bankado wata harkar damfara da ‘yan Najriya suke da hannu dumu-dumu ciki, wadda ta ce na daya daga cikin ayyukan damfara da ta taba gani a tarihinta, wasu ‘yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu.
Wata 'yar Najeriya mazauniyar birnin Los Angeles na Jahar California mai suna, Helen Bako, ta ce wannan ba shine na farko ba ko a shekarar 2011 an kama wasu mutane da dama, inda suke amfani da hanyoyi damfara guda uku wajan cutar mutane.
Helen ta kara da cewa 'yan damfarar suna amfanin da hanyar aiko da wasika ta yanar gizo na cewa waninsu ya mutu sun bar musu dukiya mai yawa suna so a taimakesu su fitar da kudaden su, wasu kuma suna aiko da hotunan su suna neman ‘yan matan da za su aura, inda suke aiko da hotunan su da wasiku daga nan sai su fara cewa su turo musu da kudi.
Sannan ta ce wannan yana shafara mutuncin ‘yan Najeriya a jihar California, kuma ta ce an cutar Amurkawa ne saboda suna da yadda da mutane shi ya sa ake yawan damfarar su.
Shima wani tsohon dan sanda a birnin New York kuma dan asalin Najeriya, Ibrahim Ahmad, ya ce 'yan Najeriya suna samu damar yin danfarar mutane ta wajan kusantar su da shiga aikin banki da kuma yiwa kamfanoni kutse don samun bayanai bankinsu.
Ibrahim ya yi kira da mahukauntan Najeriya da su tashi tsaye wajan magance wannan matsala da take bata sunan kasar a idon kasashen duniya, domin kuwa idan aka hana su to za su dawo cikin kasar ne su ci gaba da aika wannan laifuka na damfarar mutane.
Saurari cikakkiyar hirar:
Facebook Forum