Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farfesa Gambari Zai Jagoranci Tawagar Shugaba Buhari A Daurin Auren Dan Sa Yusuf


Yusuf Muhammadu Buhari da Amaryasa Zahra Nasiru Ado bayero
Yusuf Muhammadu Buhari da Amaryasa Zahra Nasiru Ado bayero

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura tawagar da ta kunshi muhimman mukarrabansa a fadar sarkin Bichi da ke jihar Kano don ta wakilce shi a bukin daurin auren dansa Yusuf Buhari, da za a yi a yau Juma’a a garin Bichi.

Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu.

A yau Juma’ah za’a yi daurin auren Yusuf Buhari dan shugaban Najeriya da ‘yar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Zahra, bayan Sallar Juma’a a fadar sarkin Bichi a Jihar Kano.

Yusuf Buhari shi ne da namiji kadai ga shugaba Muhammadu Buhari.

Sanarwar da Mallam Garba Shehu ya sanyawa hannu ta yi nuni da cewa tawagar da zata wakilci shugaba Buhari za ta kasance karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Gambari da ke zaman shugaban ma’aikatan fadar shugaban Buhari.

Sanarwar ta kara da cewa mambobin tawagar sun hada da ministan tsaro, Bashir Magashi, ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Nanono, minitsan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma ministan albarkatun ruwa, Sulaiman Adamu.

A cewar sanarwar, Malam Garba Shehu zai kasance cikin tawagar kuma bayan daurin auren zai jira zuwa ranar asabar don ya wakilci shugaba Buhari a bikin bai wa Sarkin Bichi sandar mulki.

Akwai yiyuwar gwamnoni da dama su halarci daurin auren sai kuma jiga-jigan ’yan siyasa, sarakunan gargajiya, fitattun ’yan kasuwa da sauran manyan mutane daga sassan Najeriya daban-daban.

A wani bangare kuwa, majiyoyi daga fadar shugaban kasar sun yi nuni da cewa shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki zuwa jihar Adamawa a yau Juma’a kuma tuni aka tsaurara matakan tsaro a jihar ta Adamawa.

Idan ana iya tunawa, a cikin watan Yuni ne labarin auren Yusuf Buhari ya mamaye kafaffen sada zumunta inda aka yi ta yada jita-jita kan ranar da za’a daura aurensa da yar dakin sarkin Bichi, Zahra.

Hotunan bukukuwan da aka yi don auren Yusuf Buhari da Zahra Ado Bayero kama daga na wasan Polo, bukin kawaye da aka fi sani da bridal shower, da dai sauransu suka mamaye kafaffen sada zumunta.

An dai yiwa bukin Yusuf Buhari da Zahra Ado Bayero take auren gidan sarauta da fadar shugaban kasa a kafaffen sada zumunta musamman a shafin Instagram.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG