Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Zata Soma Kai Hari Kan Kungiyar ISIS a Syria


Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande

Yau Litinin shugaban Faransa Hollande ya sanar cewa kasarsa zata soma kai hari Syria akan kungiyar ISIS

Shugaban Faransa Francois Hollande wanda kasarsa ke sintiri da jiragen sama kan Syria saboda tara bayanan asiri yace kasar zata soma kai hari da jiragen sama kan mayakan ISIS dake Syria.

Yayinda yake yiwa 'yan jarida jawabi yace da can suna sintiri da nufin tara bayanai saboda yin shirin ko ta kwana akan 'yan ta'adan Syria. Yace yanzu akwai bukatan kai hari a Syria.

Dama can Fransa tana cikin kawacen kasashen da Amurka ke jagoranta wajen kai hare hare kan kungiyar ISIS a Iraqi. Faransa ta takaita kai hare hare kan 'yan kungiyar dake Iraqi ne kawai.

To amma a karon farko shugaba Hollande ya canza ra'ayinsa. Yanzu ya fadada hare hare kan kungiyar ISIS har zuwa kasar Syria. 'Yan siyasar cikin kasar Faransan sun matsa kasar ta dauki matsayi bisa ga mummunar barazanar da suke ganin kungiyar na yiwa kasarsu..

Kafin wannan canjin matsayin Faransa na kai hari ne akan kungiyar a Iraqi kawai. Bata yadda dakarunta su kai hari kan kungiyar a Syria ba. Tana yin takatsantsan saboda bata son hare haren a Syria su karfafa ikon Shugaba Bashar al-Assad. Amma duk wannan ya kau yanzu saboda ita kungiyar ISIS ta fadada ta'adancinta daga Syria zuwa wasu kasashen.

Wani binciken bin ra'ayin jama'ar kasar Faransa da aka yi ya nuna kashi 56 cikin100 na 'yan kasar suna goyon bayan daukan matakin soji a kan kungiyar a Syria kodayake ywancinsu na ganin matakin sojin ba zai warware matasalar Syria ba.

Kawo yanzu Faransa ta bada tabbacin yin shawagi sau biyu akan Syria da jiragen sama.

Kasashe kamar su Amurka da Kanada da Turkiya da kasashen yankin Gulf suna cikin wadanda suke kai hari kan mayakan ISIS a Syria. Makon jiya ma kasar Australia tace zata shiga kawancen.

Kazalika a makon jiyan sai da jirgin Birtaniya mai sarafa kansa da kansa ya kashe mayakan ISIS biyu a Syria.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG