Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FARANSA: Dokar Haramta Wa Dalibai Mata Musulmai Amfani Da Abaya A Makarantu Ta Soma Aiki


Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron

Daga yau Litinin dokar haramta wa dalibai mata musulmi amfani da abaya a makarantun Faransa ta soma aiki, an dai dakatar da dalibai mata da suka sanya suturar daga shiga makarantun na gwamnati. 

Duk da cewa dokar haramta wa dalibai mata Musulmi sanya abaya a makarantun gwamnati ta fuskanci tirjiya daga wasu ‘yan majalisar kasar Faransa, Shugaba Emmanuel Macron, a na shi bangaren, ya tsaya tsayin daka kan dokar saboda a cewarsa, duk wata alama da ke nuna addini a makarantu da gine-ginen gwamnati ba ta da gurbi a Faransa.

Wasu dalibai a Faransa
Wasu dalibai a Faransa

Tun dai a shekarar 2004 aka sanya wa dokar hana amfami da hijabi ko dankwali a makarantun gwamnatin kasar hanu, amma Kungiyar Musulim ta CFCM a Faransa ta nuna rashin gamsuwa da dokar tana mai cewa, ba sutura kadai ce abin da ke nuna alamar addinin Musulunci ba, amma Sharif Sheridan, wani dan jarida mai zaman kansa a Faransan, ya ce akwai bukatar mahukuntan na Faransa su sake nazari tun da tsarin dimokaradiyya ake bi a kasar.

Wata daliba a Faransa
Wata daliba a Faransa

A baya dai Ministan Ilimi Gabriel Attal ya ce, sun dauki matakin ne domin bai kamata ana iya tantance addinin mutum da zarar an kalleshi ba, hasali ma tun a karni na 19 Faransa ta haramta duk wata alama da ke nuna addini kamar tambarın Yesu Almasihu na Kristoci.

Saurari rahoton Ramatu Garba Baba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG