Tsoron da ake nunawa akan tafiyar hawaniyar da bunkasar tattalin arzikin China ke yi da rashin sanin tabbas akan harkokin siyasar kasar Girka da kuma rashin sanin tabbas akan shirye shiryen da ake yi ba kara kudi ruwa da hukumomin Amurka suke tunanin yi sun girgiza masu zuba jarri, al'amarin daya sa aka shiga gwanjon sayar da hanaye jarri a jiya Juma'a.
Kasuwanin hanayen jarri anan Amurka sunyi kasa da kashi uku daga cikin dari a lokacinda aka rufe kasuwanin a jiya Juma'a. A turai kuma kasuwanin suma sun fadi da kashi uku daga cikin dari, haka suma muhimman kasuwanin hanayen jarri a Asiya sunyi mugun faduwa.
Fargabar da ake nunawa akan bunkasar tattalin arzikin China dake kasa tana dabo, kasa ta biyu a bunkasar tattalin arziki yasa farashin mai faduwa a kasuwanin duniya. Yanzu ana sayar da garwar mai akan dala arba'in, farashi mafi kakanci da aka gani cikin shekaru shidda da suka shige
.
Bunkasar da tattalin arzikin China ke yi cikin shekaru goma da suka shige ne ya janyo ci gaban da aka a kasuwanin makamashi da wasu hajjan da ake sayarwa a kasuwani duniya.
To amma kuma wani sabon rahoto ya nuna gagarumin komadar tattalin arzikin China maimakon bunkasa.
Tuni gwiwar masu zuba jarruruka ya yi sanyi a saboda rikici a kasuwanin hanayen jarrin China da kuma rage darajar takardun kudin kasar daya bada mamaki.