Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aure Daga Wata Kabila Daban!


A shirin mu na karshen wannan makon, mun sami zantawa ne da samari da 'yan mata akan aure tsakanin kabilu daban daban, koda shike jama'a da dama na cinkin wannan hali musamman ma matasa kamar yadda masana suka fada.

Aure tsakanin kabilu daban - daban na da matukar fa'ida da kuma amfani musamman wajan hada kan kasa da al'umma da kuma addinai daban daban a fadin duniya.

Kamar yadda matasan suka bayyana wa dandalin voa, ilimin zamani da tafiye tafiye da kuma sauran abubuwa makamantan su da ke da alaka da zaman tare ya sa auren gamayya ya zamo tamkar wutar daji, koda shike a ceawr su, abin alfahari ne ga kowace al'uma domin hakan na haifar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin kabilu.

ku saurari cikakkiyar hirar a dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG