A tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar Amurka, wanene yafi wani hawan mota mai tsada? Dukkan wadanda ke neman kujerar shugaban kasar Amurka na shekarar 2016, babu talaka a cikin su, kowannen yayi wani abun da za’a iya duba mishi a tsawon rayuwa.
Dr. Ben Carson, wanda yake likitan kwakwalwa ne, yana hawan 2012 BMW 335i, wanda ya bayyana dalilin da yasa yake son motar da cewar, motar ta ceci ranshi, a lokacin da wasu motoci 2 suka fado mishi amma koda aka fito da shi bai ji ciwa ba.
Chris Christie, gwamnan jihar New Jersey, yana hawan motar kamfanin GM, duk dai da cewar an hana shi tuka mota, bayan ya zamo gwamna, amma a wasu lokutta yakan tuka kanshi zuwa wasu gurare don nishadi.
Ita kuwa Hillary Clinton, ta kwashe fiye da shekaru 20 bata tuka mota da kanta ba, yanzu haka duk ranar da zata bukaci tuka mota sai ta duba ranar da akace lasisinta ya kare, don bata amfani da shi. Dalilin kuwa da yasa bata tuka mota shine saboda irin aikin da ta tsinci kanta ciki. Tace a shekarar 1963 tana iya tuna motar ta ta farko, lokacin da take jami’a tana karatun lauyanci. Ta siya motar a kan kudi $120 harma a loacin sanyi, tana iya tuna wata rana da motar ta taki tashi, sai a kace mata batiri ne don haka tun daga ranar idan dare yayi, idan zata shiga bacci sai ta dinga daukar batirin motar, tana shiga da shi cikin dakin ta, don kada yayi sanyin da ba zai iya tada motar ba da safe.