Kungiyar yaki da miyagun kwayoyi da ake kira FADEA a takaice ta bukaci 'yan siyasa da su daina amfani da matasa wajen basu miyagun kwayoyi, domin amfani da su wajen bangar siyasa da tada zaune tsaye a wani yunkuri na cimma wasu bukatun su.
Shugaban Kungiyar ta FADEA Malam Muktar Illiyasu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir a birnin kano.
Muktar ya ce babban burin kungiyar bai wuce kaddamar da kungiyoyi ko tsangayu a makarantun sakandare domin nusar da matasa tun daga tushe akan kawar da matsalolin shaye-shayen miyagun kwayoyi, abinda ya kai su ga bude tsangayu a unguwanni da dama a fadin Najeriya.
Ya ce, a yanzu sun fara ne da kafa kananan kungiyoyi a wasu sassan Najeriya don wayar da kan al’umma akan illar shan kwayoyi da zummar daukar wasu daga cikin irin wadannan matasan da iftila’in shan kwaya ya jefa su cikin halin kaka-na-kayi domin ceto su.
Muktar ya bukuaci al’umma da ta daina kyamatar masu shan kwaya, maimakon haka ta karbe su hannu biyu-biyu ta hanyar jansu kusa domin nusar da su irin illolin da shan kwaya ke haifarwa.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum