Kafar sada zumunta ta Facebook ta rufe daruruwan shafukan yanar gizon masu alaka da jam’iyyun siyasar India, ko kuma sojojin kasar Pakistan, saboda abin da kamfanin ya kira “shiryayyun harkoki na bogi da kuma yada bayanan karya.”
An bankado wadannan shafukan na Facebook da Instagram ne, ta wajen binciken da aka yi kan shafukan sada zumuntar a yankin, a gabanin zabukan da za a yi a India.
Babbar kafar sada zumuntar, ta ce ta ankara da aika-aikar wasu masu amfani da ita ne, bayan wata tabargazar da ta nuna cewa wani kamfanin nazarin bayanai mai suna Cambridge Analytica, ya yi amfani da bayanan da ya kalato daga miliyoyin masu amfani da shafukan Facebook, saboda ya jirkita tsarin yakin neman zabe a kasashe da dama, ciki har da Amurka.
A 'yan kwanakin nan, kamfanin na Facebook na fuskantar suka kan yadda ake amfanin da shafinsa wajen yada labaran bogi ko kuma wani abu da jama'a bai kamata su gani ba.
Facebook Forum