Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Da Ta Burtaniya Sun Kalubalanci Kamfanonin Fasaha


Firayin Ministar Birtaniya Theresa May, da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, sun hada kai don yakar kamfanonin fasaha da kuma tabbatar da ganin sun tashi tsaye wajen yaki da yada akidar ta’addanci a kafofin sadarwa.

Birtaniya da Faransa na fuskantar kalubale wajen yaki da ‘yan ta’addar cikin gida, kasancewar ire-iren hare-haren ta’addanci da aka kai musu irin na biranen Paris da Manchester da kuma Nice.

Ranar Talatar da ta gabata ne May ta ziyarci Paris, domin gudanar da wani taro kan hanyoyin dakile ta’addanci da kuma maganar ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

Ta ce manyan kamfanonin fasaha basa yin abin da ya kamata wajen tabbatar da ganin sun hana masu tsatstsauran ra’ayi amfani da kafafensu. Macron ya yi kira ga sauran kasashen Turai musamman ma Jamus da ta shiga wannan yunkuri na yakar yada akidun ta’addanci a yanar gizo.

Kamar yadda May ta ce, idan har kamfani bai dauki matakin kare yada akidar ta’addanci ba a dandalinsa, yana iya fuskantar tara.

Yanzu haka a Birtaniya an samar da wata doka da ta baiwa jami’an tsaro ikon duba tarihin amfani da yanar gizo na kowannne mutum a kasar.

Dokar kuma ta bukaci kamfanonin sadarwa da su rika ajiye tahirin abubuwan da mutane su kayi a yanar gizo har na tsawon shekara guda, inda suke bude kundin ajiye bayanai ga kowanne ‘dan kasar, wanda hakan yasa ake ganin zai iya zama hatsari idan ya fada hannun masu kutse ko aka kwarmata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:33 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG