Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta dauki matakin magance matsalar farashin kudaden waje da ake samu a farashi daban-daban a kasuwar canji.
Buhari wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya kaddamar da taron Bunkasa Tattalin Arzikin kasa a juko na 28 da aka yi a Abuja.
Shugaban na Najeriya ya yi la’akkari da yadda wannan matsala ta samun kudaden ketare a farashi daban-daban take haifar da cikas ga tattalin arzikin kasa.
Ya kara da cewa akwai bukatar a bunkasa fannin samun kudaden ketaren da yadda ake sarrafa su, yana mai cewa gwamnati na da damar da za ta iya kula da dukkan fannonin biyu.
Ana dai samun dala da saraun kudaden ketare a farashi daban-daban a kasuwar canji, lamarin da ke sa darajar naira na faduwa saboda karancin kudaden.