Dan wasan kasar Uruguay Edison Cavani, ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyu da kungiyar Valencia a ranar Litinin.
Dan shekara 35, Cavani bai samu kungiya ba, tun bayan da kwantiraginsa ya kare da Manchester United a karshen kakar wasan da ta gabata.
A baya, dan wasan gaban ya taba bugawa Paris Saint Germain, Napoli da Palermo.
Cavani na filin wasan Valencia na Mestalla a lokacin da Atletico Madrid ta lallasa kungiyar da ci 1-0 a ranar Litinin a gasar La Liga.
Kungiyar ta yi nasarar lashe wasa daya ne cikin wasanninta uku na farko.