Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Jaddada Muhimmancin Kiwon-Yawo


ECOWAS
ECOWAS

Kwamitin nazarin Noma na kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS ya karfafa bukatar bunkasa kiwon Dabbobi ta hanyar ratsa dazuka da ke yankin.

Jami’an kwamitin sun ce nau’o’in dabbobin da a ke kiwo a yankin musamman shanu na taimakawa wajen bunkasar lafiyar kasar Noma ta takin gargajiya, yaki da hamada da raya burtali da kuma cudanyar jama’ar Afirka daga sana’o’i daban-daban.

Kwamitin ya lura ana samun fitinar manoma da makiyaya don sare dazuka da kafa gonaki a kan burtali.

Gwamnatin Najeriya ta bullo da wani tsari na warewa Makiyaya Dazukan da za su yi kiwo da tuni hakan ya samu karbuwa a Jihohin Arewa da dama.

A kan samu rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya daidai lokacin damuna matukar makiyaya su ka kyale dabbobi su ka shiga gonaki ko kuma lokacin tafiya kudanci daga arewaci don neman ciyawa da a ke kira mashekari.

Saurari cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-hikaya, cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG