Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Da Aka Gargadi Shugaba Conde Kan Batun Ta-zarcensa – Ibn Chambas


Mohamed Ibn Chambas (VOA/Ginette Fleure Adandé)
Mohamed Ibn Chambas (VOA/Ginette Fleure Adandé)

Chambas ya nuna fargabarsa kan yadda nahiyar Afirka musamman yankin yammaci yake fadawa kangin juyin mulki.

Tsohon wakilin na musamman ga Babban Sakataren Majalisar Dikin Duniya, Mohamed Ibn Chambas ya nuna takaicinsa bisa juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Guinea a ranar Lahadi.

Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, Chambas ya nuna fargabar yadda nahiyar Afirka musamman yankin yammaci yake fadawa kangin juyin mulki.

Chambas, wanda har ila yau shi ne tsohon shugaban kula da ofishin Majalisar Dinkin Duniya a yammcin Afirka da Sahel, ya shawarci kasashen Afirka da ke son su sauya kundin tsarin mulkinsu, musamman fannin da ya shafi wa’adin shugaban kasa, su tabbata sun samu goyon bayan daukacin jama’a kafin su yi wannan kwaskwarima.

Alpha Conde
Alpha Conde

A cewar Chambas, kungiyar ECOWAS da ta tarayyar Afirka ta AU, sun yi tsayin daka wajen shawo kan shugaba Alpha Conde wajen ya janye shirinsa na sauya kundin tsarin mulkin kasar a watan Maris din da ya gabata amma ba ji ba, matakin da ‘yan adawa suka ce ya yi amfani da shi wajen yin ta-zarce a wa’adi na uku.

Sai dai a karshe ya ce, yana fatan ganin kungiyar ta ECOWAS ta jaddada matsayarta ta nun aba-sani-ba-sabo ga sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea tare da kiran da su saki shugaba Conde.

Kanar Colonel Doumbouya, da ya jagoranci juyin mulkin Guinea
Kanar Colonel Doumbouya, da ya jagoranci juyin mulkin Guinea

A watan Oktoba shugaba Conde ya lashe zabe a karo na uku bayan da ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima a watan Maris, abin da ya ba shi damar sake tsayawa takara duk da cewa ya kammala wa’adinsa na biyu.

Wannan mataki ya haifar da rudani da zanga-zanga a duk fadin kasar.

A ranar Lahadi, wasu sojoji karkashin jagorancin Col. Mamady Doumbouya suka kwace mulki a hannun Conde.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG