Tawagar likitoci daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, sun isa demokaradiyar jamhuriyar Congo domin yaki da cutar Ebola, yayin da jami’an gwamnati a yankin suke iya kokarinsu su na dakile anobar cutar.
Ministan kiwon lafiya a Najeriya Isaac Adewole ya fada a jiya Laraba cewa, Nigeria ta kara karfafa binciken lafiyar baki da suke zuwa daga kasar DR Congo kana kuma Najeriya na nazarin tura likitoci zuwa kasar su taimaka wurin shawo kan yaduwar cutar Ebola.
Hukumar kiwon lafiya ta WHO ta tura likitoci na fanni dabam dabam da suka hada da masu jinyar wadanda suka harbu da masu hana yaduwar cuta zuwa DR Congo.
Facebook Forum