Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Ta Sake Barkewa A Kasar Dimokradiyar Kwango


Shugaban Dimokradiyar Kwango Joseph Kabila
Shugaban Dimokradiyar Kwango Joseph Kabila

Kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta ce an samu sabuwar matsalar barkewar cutar Ebola a yankin da ake kira Bikoro da ke Lardin Equarteur, bayan da mutane 17 suka mutu daga wata cuta da ake tunanin cutar ta Ebola, inda tuni har an tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu ne sanadiyar cutar.

A jiya Talata, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da cewa kasar ta Congo na fama da sabuwar matsalar barkewar cutar ta Ebola, inda ta ce tuni ta tura Dalar Amurka Miliyan daya daga asusunta na taimakon gaggawa domin a yaki cutar.

Hukumar lafiyar ta Duniya, ta kuma ce a cikin makwannin biyar da suka gabata ne, aka samu mutane 21 da ake zaton suna fama da zazzabin cutar nan mai haifar da kwarara jini a yankin, kuma daga cikinsu ne 17 suka mutu.

Hukumar lafiyar ta kara da cewa za ta tura kwararru daga fannonin kiwon Lafiya daban-daban zuwa yankin, nan da wasu kwanaki masu zuwa, sannan ta ce ta yi yakewu ga sauran kasashen da ke makwanbtaka da kasar ta Congo kan barkewar cutar.

Lokaci na karshe da aka ji bullar cutar ta Ebola a kasar ta Congo a bara ne, inda mutane hudu suka mutu daga cikin mutane takwas da suka kamu da ita.

Wannan kume shi na karo na tara da ake samun barkewar cutar, tun bayan da aka gano kwayar cutar a shekarar alif-dari-tara-da-saba’in-da-shida a wani kogi da ake kira Ebola.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG