Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Shugaba A Kasar Poland


Sabon shugaban kasar Poland Bronislaw Komorowski, yayi alkawarin zai kokarta hada kan al’ummar kasar wadanda suka samu mummunar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa.

An rantsar da sabon shugaban kasar Poland, Bronislaw Komorowski, inda yayi alkawarin hada kasar da ta samu mummunar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa. A yau jumma’a, Mr. Komorowski yace zai yi aiki tare da majalisar dokoki da wasu cibiyoyin gwamnati da kuma jam’iyyun adawa kan muhimman batutuwa ciki har da batun tattalin arzikin kasar. Komorowski mai shekaru 58 da haihuwa, shi en ya lashe zaben fitar da gwani na watan Yuli da kashi 53 cikin 100, inda ya doke abokin takararsa dan ra’ayin rikau, Jaroslaw Kaczynski, wanda bai halarci bukin rantsar da sabon shugaban a yau jumma’a ba. Kaczynski yayi kokarin ya gaji dan’uwansa shugaba Lech Walesa wanda ya mutu tare da wasu jami’an Poland su 95 a lokacin da jirginsu ya fadi a kasar Rasha a watan Afrilu. Jami’an Poland sun yi shiru na wani dan lokaci kafin a fara gudanar da bukin na yau, kuma shugaba Komorowski ya karrama mutumin da ya gada a cikin jawabin da yayi.

XS
SM
MD
LG