Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Drogba Ya Tsaya Takarar Shugaban Hukumar Kwallon Ivory Coast


Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara
Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara

Shahararren da wasan kasar Ivory Coast Didier Drogba ya tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar.

Drogba mai shekaru 42 da haihuwa, ya gabatar da takardun tsayawa takara da ya cike a hukumance tare da rakiyar daruruwan magoya baya da suka yi jerin gwano, inda ya kasance mutum na 4 da ke takarar shugabancin hukumar ta kwallon kafar kasar.

To sai dai babu tabbacin cewa tsohon gwarzon dan kwallon na Afirka zai kasance a cikin ‘yan takara na karshe na zaben da za’a gudanar a ranar 5 ga watan Satumba mai zuwa.

Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara
Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara

Ko baya ga sharadin samun goyon bayan kungiyoyi 3 daga cikin 14 da ke fafata gasar Ligue 1 da kuma kungiyoyi 2 da ke buga kananan gasanni, wajibi ne kuma Drogba ya sami amincewa da goyon bayan daya daga cikin rukunnan kungiyoyi na musamman, kamar masu horar da ‘yan wasa, likitoci, gungun ‘yan wasa na da da na yanzu da kuma na alkalan wasa.

Wadannan rukunnan ba su kai ga fitowa fili suka bayyana dan takarar da za su goyi baya ba, haka kuma wata hukumar zabe ce za ta soma tantance ‘yan takarar kafin su iya tsayawa takara a zaben hukumar.

Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara
Didier Drogba ya gabatar da takardun tsayawa takara

Ana sa ran sakamakon tantance ‘yan takarar na karshe zai fito nan da kwanaki biyar, in ji mai magana da yawun hukumar kwallon kafar kasar.

Drogba ya bugawa kasar wasa a gasanni 3 na cin kofin duniya, kana kuma sau 2 yana bugawa kasar wasa tana lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Tauraruwarsa ta haska sosai har ya yi suna a zamansa kungiyar Chelsea ta Ingila, inda ya lashe gasannin Premier da Zakarun Turai.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG