Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Yadda Matan Najeriya Zasu Tinkari Zaben 2023-Kashi Na Daya, Agusta, 11, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Banda batun harkokin tsaro, daya daga cikin batutuwan da su ka fi daukar hankali a Najeriya shi ne batun zaben 2023, da mata su ke kara daura damara domin ganin a wannan zaben, sun sami kyakkyawan wakilci.

Duk da yake hakar mata da dama da suka nemi jam’iyunsu su tsaida su takara bata cimma ruwa ba, matan na kokarin fargar da ‘yan’uwansu domin ganin kalilan da su ka sami nasara a zaben fidda gwani sun kai labari.

Bakin da shirin Domin Iyali ya gayyata
Bakin da shirin Domin Iyali ya gayyata

A wannan makon, shirin ya karbi bakuncin Hajiya Khadija Abdullahi Iya ‘yar takarar gwamnan jihar Naija ta jam’iyar AFGA, da Mrs Dorathy Nuhu Aken ‘Ova wadda ta nemi a tsaida ita takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar SDP, sai kuma Hajiya Mariya Ibrahim Baba ‘yar siyasa kuma ‘yar gwaggwarmaya, da kuma dan siyasa Sa’iidu Gombe.

Saurari kashin farko na tattaunawar da Shamsiya Hamza Ibrahim ta jagoranta:

DOMIN IYALI: Yadda Matan Najeriya Zasu Tinkari Zaben 2023-Kashi Na Daya
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:45 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG