Idan kuna biye da mu, Shirin Domin Iyali yana nazarin ci gaban da ake samu a kasashen duniya dangane da samun mata a manyan madafun shugabanci da ya hada da zaben mace a mataimakiyar shugaban kasar Amurka da kuma ‘yar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da ta zama macen farko kuma bakar fata ta farko a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.
A ci gaba da nazarin yadda mata a kasashen nahiyar Afrika za su dora a wannan ci gaban da ake samu, yau ma muna tare da Shugabar gamayyar kungiyoyin mata a Najeriya Madam Gloria Laraba Shoda, da hajiya Balaraba Mohammed shugabar kungiyar Mata Fulani ta babban birnin Tarayya Abuja, da kuma Hajiya Sa’adatu Ahmed Bustani mazauniyar birnin tarayya Abuja.
A yau bakin sun maida hankali kan yadda mata za su iya shawo kalubale da ke zama kadangaren bakin tulu a yunkurin cima wannan gurin.
Saurari kashi na biyu na tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta: