WASHINGTON, DC —
Bayan Amurka ta yi tarihi da zaben mace ta farko a matsayin shugabar kasa, da kuma zaben ‘yar Najeriya Ngozi-Okonji-Iweala macen farko kuma bakar fata ta farko a matsayin shugabar Kungiyar cinikayya ta duniya, mata na kara samun kwarin guiwar cimma burinsu na ganin an dama da su a harkokin mulki.
Maudu’in da Shirin Domin Iyali ya yi mukala a kai ke nan a wannan shirin. Domina bada gudummuwa ga shirin mun gayyaci Shugabar gamayyar kungiyoyin mata a Najeriya Madam Gloria Laraba Shoda, da hajiya Balaraba Mohammed shugabar kungiyar Mata Fulani ta babban birnin Tarayya Abuja, da kuma Hajiya Sa’adatu Ahmed Bustani mazauniyar birnin tarayya Abuja.
Saurari tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta: