A yau shirin Domin Iyali ya koma kan nazarin da mu ka fara dangane da batun karuwar mace macen aure da ake fuskanta a dukan jihohin Jamhuriya Nijar inda bayanai ke nuni da cewa, an sami mutuwar aure sama da 3000 a shekarar da ta gabata a birnin yamai kawai, yayinda a jihar Agadas rahotanni ke nuni da cewa, a kowacce rana akan sami karafe korafen neman kashe aure a kalla shida, a kuma raba a kalla uku daga ciki.
Rahoton ya kuma nuna cewa, shekara ta 2021 ce shekarar da aka fi samun yawan mace macen aure a Jamhuriyar Nijar baki daya
Bakin da muka gayyata domin neman sanin masababin wannan lamarin da kuma hanyar magance ta su ne, Hajiya Halima Sarmay dattijiya kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara, da Malan sani Sabiou Souleyman shugaban kungiyar addinn Islama ta Aisef, da kuma Falmata Moctar Taya shugaban kungiyar matasa.
Saurari tattaunawar da Souley Moumouni Barma ya jagoranta.