Washington, Dc —
Duk da yake yunkurin mata da dama da su ka nemi tsayawa takara ya gamu da cikas a lokacin zabukan tsaida ‘yan takara, kalilan da suka haye wannan matakin na ganin idan aka zabe su, za su yi iyakar kokari domin ganin sun shawo kan matsaloli a da suka abbadabi iyali.
Shirin na yau, ya karbi bakuncin Hauwa Lawal ‘Yar Gata ‘yar takarar Majalisar dokoki a jihar Katsina, da kuma Sa’afatu Labo mai takara a jihar Zamfara, wadanda suka bayyana burin da su ke neman cimma da ya sa su ka tsaya takara, da kuma kalubale da su ke fuskanta.
Saurari tattaunawar da wakilin Sashen Hausa Sani Shu'aibu Malumfashi ya jagoranta: