Washington, dc —
A ci gaba da nazarin matsayin takarar mata a babban zaben da za a gudanar a Najeriya, da kuma abinda za a iya yi a cike wagegen gibin da ke akwai tsakanin takarar maza da ta mata, bakin da muka gayyata , Hajiya Binta Musa shugabar kungiyar hadin kan mabiya addinai dabam daban reshen jihar Plato, da Ambassador Rhoda Godwill Jahota, shugabar kugiyar mata Kirista a jihar Plato, da Dorcas Lenkat Yusuf shugabar gamayyar kungiyar ma’aikatan gwamnati a jihar Plato mai barin gado, sai kuma Ambassada Ridwan Jimat Imam, malami karkashin kungiyar Jam’atu Nasril Islam, sun bayyana abinda ya banbanta takarar mata da ta maza a siyasar Najeriya.
Ga ci gaban tattaunawar da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji ta jagoranta: