Washington, DC —
Ga wadanda suke bibiyar shirin, mun fara wannan shekarar ne da neman jin inda al’umma ke son ganin hukumomin kasar sun maida hankali a kai, muka kuma yi alkawarin haska fitila kan wadansu daga cikin bangarorin idan ta kama.
Tuni aka ce maganin mantuwa, kafin sake haska fitila kan wadannan bangarorin, bari mu tuna maku da abinda wadanda Muryar Amurka ta yi hira da su suka shaidawa shirin Domin iyali, faro daga Najeriya, inda a farkon wannan shekarar, banda matsalar tsaro da tsadar rayuwa, abinda ya fi daukar hankalin ‘yan Najeriya shine,janye farashin man fetir da Bola Ahmed Tinubu ya sanar bayan daukar rantsuwa.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna