Masu ruwa da tsaki a taron na ranar ruwa ta duniya mai taken ”gaggauta kawo sauyi” wanda aka yi a Abuja, sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki don samar da yanayi mai dorewa a fannin samun tsaftataccen ruwan sha da na amfanin yau da kullum musamman ga yara, da aikin samar da abinci ga kowa, da la’akari da bukatun ruwa a gidaje da sauran wurare.
A yayin jawabin da ta yi bayan taron na masu ruwa da tsaki, Mrs. Nweke wacce ta wakilci babban sakataren ma’aikatar ruwa ta tarayya, ta ce bikin na bana ya mayar da hankali ne a kan fafutukar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen linka kokarinsu, da zuba isassun kudadden da ake bukata don aikin samar da tsaftataccen ruwan sha, da samar da kayayyakin aiki, da bada bayanai da kuma kirkire-kirkire don ganin an cimma dukkan amfanin da za a iya samu na ruwa bayan rage yawan matsalolin da ke tattare da rashin tsaftataccen ruwan sha.
A nata bangaren a yayin gabatar da jawabi a lokacin taron, jagorar shirin WASH, da ke fafutukar kula da tsaftar muhalli na asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF a Najeriya, Dakta Jane Bevan, ta ce ba a sami wani gagarumin ci gaba ba a yanayin samar da tsaftataccen ruwan sha da na amfanin yau da kullum, sakamakon yadda ba a iya samun dorewa a tsare tsaren da aka shirya ba, abinda ke nufin kaso uku bisa hudu na ‘yan Najeriya ba sa samun tsaftataccen ruwan sha.
Ta na mai cewa kamata ya yi a ba da karfi wajen zuba kudaden da ake bukata a fannin da kuma sa ido akan tsare-tsaren samar da ruwa da ke kasa don ganin an cimma nasara.
A wani bangaren kuma, masani a fannin muhalli da albarkatun kasa da ke aiki tare da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO, Seyi Fabiyi, ya ce ruwa na da muhimmanci ga manufofin FAO saboda yadda kaso saba'in da biyu cikin dari na janyewar ruwa ana amfani da su ne a fannin aikin noma kuma tsarin abinci ya dogara sosai kan albarkatun ruwa.
Kwamitin ofishin bayanai na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma mika rahoto akan ababen da ya gano don inganta aikin samar da tsaftataccen ruwan sha ga gwamnatin Najeriya.
Kazalika, ma'aikatar ruwa ta tarayya ta bai wa wasu matasa mata ‘yan sakandare lambar yabo saboda jajircewarsu wajen aikin tsaftacce makarantarsu da ke unguwar Dutsen Alhaji a Abuja.
To ko yaya wasu ‘yan Najeriya ke ganin muhimmancin samun tsaftataccen ruwan sha da na bukatar yau da kullum? Khadija Hassan Sani, wacce ta ce ruwa na da matukar muhimmanci ga rayuwar dan adam na yau da kullum, ta ce idan babu ruwa ba yadda mutum zai iya tafiyar da rayuwarsa yadda ya kamata.
Masu ruwa da tsaki a fannin samar da tsaftataccen ruwan sha dai sun bayyana cewa kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin da suka shafi samar da ruwa, kuma yanzu lokaci ya yi da za a dauki mataki ta hanyar zuba kudi a fannin samar da ruwa, tsaftar muhalli, ba wai kawai don batun kare lafiyar yara a yau ba, har ma da samar da makoma mai dorewa ga tsararraki da inganta rayuwarsu.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf: