Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Baiwa Ministansa Hutun Wata Guda Domin Ya Yi Takara


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Kimanin watanni uku da suka gabata ne hukumar zabe ta Najeriya INEC ta fitar da jadawalin zaben shekara mai zuwa ta 2019 wadda ya kunshi zaben cikin gida na Jam’iyyu domin fitar da ‘yan takara a matakai daban-daban. Sai dai masu kula da lamura na ganin ‘yan siyasa da jam’iyyun su na neman wuce gona da iri wajen gudanar da harkokin da suka shafi zaben na badi.

A wata sabuwa kuma, ‘yan najeriya na ci gaba da mahawara akan hutun wata guda da shugaban Muhammadu Buhari ya baiwa ministan raya ma’adinai na kasar, Dr Kayode Fayemi domin ya nemi takarar gwamnan jihar Ekiti da za’ayi a ranar 14 ga watan Yuli.

To amma Dr Nasiru Adamu Aliyu, malami a tsangayar nazarin aikin lauya ta Jami’ar Bayero Kano ya fada cewa, da shugaban kasar da ministan ba su bi doka ba, har yana fadin ya za'ayi mutum na kan aiki a bashi hutu ya tsaya takara, hakan sam bai yi daidai ba.

Jadawalin dai ya nuna Jam’iyyu za su kammala zabukan fitar da gwani yayin da za a yi zabukan gama gari a cikin watan Fabareru na badi.

Yanzu haka dai ‘yan siyasa, kama daga masu rike da gwamnati zuwa wadanda ke neman madafun iko a matakai daban daban, sun dukufa wajen al’amura masu nasaba da zaben badi, kama daga taruka a kafofin labaru zuwa taruka a ciki da wajen Najeriya, al’amarin da masana ke ganin ya ci karo da dokokin kasa.

Dr Nasiru ya bayyana cewa akwai banbaci tsakanin neman tsayar da mutun takara a cikin jam'iyya da kuma a waje, doka ta hana tsayawa takara amman bata hana kamfen na cikin gida ba, kuma hakan ya sabawa doka.

Masu kula da al’amura dai na ganin wannan zumudi da ‘yan siyasar najeriya ke nunawa game da zabukan shekara mai zuwa nada alaka da muradin samun madafa a gwamnati saboda rashin gamsuwa da yadda mulkin demokaradiyyar kasar ke Garawa a yanzu.

To amma Malam Abbati Bako guda cikin masana a fagen siyasa na cewa matsalar itace bin ka'idoji, kula da hakan shine yake taimaka ci gaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG