Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diddy Da Cassie Sun Sasanta


Diddy, hagu, da Cassie, dama, a shekarar 2018 a New York
Diddy, hagu, da Cassie, dama, a shekarar 2018 a New York

Cassie ta shigar da karar Diddy a gaban kuliya inda ta yi zargin ya yi mata fyade tare da cin zarafin ta, ciki har da duka.

Fitaccen mawakin Amurka, Sean Combs da ake kira Diddy ya sasanta da mawakiya Cassie wacce ta maka shi a kotu a makon nan.

Cassie ta shigar da karar Diddy a gaban kuliya inda ta yi zargin ya yi mata fyade tare da cin zarafin ta, ciki har da duka.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa Diddy da Cassie sun sasanta ba tare da kotu ta sa hannu ba.

A ranar Juma’a lauyan Cassie ya fitar da wata sanarwa, kwana guda bayan da Cassie wacce asalin sunanta Casandra Ventura ta shigar da karar.

Sanarwar ta ce Diddy da Ventura sun cimma matsaya “da ta gamsar da kowa.”

Ba a dai fitar da wani bayani da ke nuna matsayar da aka cimma ba, amma Ventura da Diddy duk sun sanar da cewa sun kai ga sasantawa.

A da, Diddy da Cassie saurayi ne da buduwar wadanda suka fara mu’amulla tun a shekarar 2005.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG