Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Golden Eaglets Yayi Abin Tarihi


Dan wasan tsakiya na Golden Eaglets na Najeriya, Samuel Chukwueze, yayi abin tarihi domin kuwa dakika 25 kacal ya dauka daga fara wasa kafin ya jefa kwallo a ragar ‘yan wasan kasar Chile, a gasar cin kofin duniyar da ake yi a kasar ta Chile.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta fada a shafinta na intanet cewa Chukwueze shine na uku a tarihin gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta samari ‘yan kasa da shekara 17 da ya jefa kwallo cikin dan kankanin lokaci, ma’ana ‘yan wasa 2 kacal ne a duniya suka fi shi saurin jefa kwallo a wannan gasa tun lokacin da aka fara yinta a shekarar 1985.

'Yan wasan sun hada da Fabinho na Brazil a gasar da aka yi a Koriya a 2007 wanda ya jefa kwallo cikin dakika 9, sai kuma wani dan kasar ta Brazil shi ma Celso wanda a gasar da aka yi a Peru a 2005 ya jefa kwallo cikin dakika 14 da fara wasa.

Da aka fada masa wannan abin tarihin da yayi, sai Chukwueze ya rike baki yana murmushi, sannan y ace, ban san da wannan ba, amma kuma abin farin ciki da karramawa ne sanin cewa sunana ya shiga cikin tarihin gasar cin kofin duniya. "Kai wannan abin alfahariu ne in ji shi.”

A bayan wannan kwallon farkon ma, Chukwueze ya jefa ta biyu daga bisani, sannan yana da hannu a wasu kwallaye biyun da aka jefa a ragar ‘yan kasar ta Chile. Kwallo ta biyar ce kawai bashi da hannu a ciki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG