An kammala ciniki tsakanin kungiyar kwallon Kafa ta Liverpool ta kasar Ingila da takwararta Barcelona, ta dake Spain, kan sayen dan wasan tsakiya na liverpool Philippe Coutinho.
Tuni dai Kungiyar Liverpool ta amince da sayar da dan wasanta Philippe Coutinho, ga kungiyar Barcelona kan kudi fam miliyan £145, kimanin yuro miliyan €160 Dalar Amurka miliyan $192.
Coutinho ya rattaba hannu a yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyar da rabi a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda a yanzu haka ya zamo dan wasa mafi tsada a yankin Burtaniya. Haka kuma ya kasance dan wasan da yafi duk wani dan wasa tsada a kungiyar ta Barcelona.
Kuma shine dan wasa na biyu mafi tsada a duniya tun bayan lokacin da Neymar, ya koma kungiyar Paris Saint-Germain, daga kungiyarsa ta Barcelona a kan zunzurutun kudi yuro miliyan €222.
Tun a farkon kakar wasan bana ne dai kungiyar ta Barcelona ta yi ta kokarin ganin ta dauko dan wasan, Philippe Coutinho, Amma lamarin ya ci tura, sai a watan janairu nan.
Real Madrid, ta ce ta yi shirin Saka kudi fam miliyan £177 ga Philippe Coutinho, kafin ya cimma yarjejeniya da Barcelona, akan kudi fam miliyan £145.
Sai dai yanzu Kungiyar Real Madrid, ta ce babban abinda yake gabanta kan sayen zaratan ‘yan wasa shine dauko dan wasan tsakiya na Chelsea Eden hazard da kuma mai tsaron ragar ta Courtious. Sa’annan kuma tana jira kan batun tattaunawa da dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane.
Facebook Forum