Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBYA: Saif al-Islam Gadhafi Yana Son Shiga Takarar Shugaban Kasa


 Saif al-Islam Gadhafi
Saif al-Islam Gadhafi

Saif al-Islam Gadhafi, dan marigayi Moammar Gadhafi mai kishin kasar Libya, ya bayyana shirin yin takarar shugabancin kasar wadda Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen yamma suke matsin lamba a gudanar da zaben a watan Disamba.

Ba a sake ganin Saif al-Islam Gadhafi, a bainar jama'a ba tun lokacin da 'yan tawayen da suka tsare shi suka sake shi a shekarar 2017.

Shigar Saif zaben bai gamshi jami'an diflomasiyya na Yamma da masu ba da shawara kan dimokiradiyya na kasa da kasa ba, wadanda suke cewa a yanzu haka Libya na da isassun manyan matsalolin da za a shawo kansu ba tare da an hada da dan Gadhafi ba, mutum mai matukar farin jinin kuma mai fada-a-ji.

Saif, wanda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ke nema kan laifukan yaki, ya yi magana ta hanyar masu shiga tsakani da kafofin yada labaran Yammacin Turai. Wata babbar jaridar Amurka ta yi hira ta musamman da shi, wanda aka shirya za a buga a watan gobe, a cewar masu shiga tsakanin.

A hirarta da Muryar Amurka, Claudia Gazzini ta kungiyar International Crisis Group, wata cibiyar bincike a Brussels ta ce,“Har yanzu ba a fayyace ko a zahiri zai sa kansa a matsayin dan takara ba. A yanzu dai sai idan na ji shi ko na gan shi kan bidiyo ya ambata sannan zan yarda, ”in ji

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG