Wannan shirin ya kasance dalilin da ya sa yawancin 'ya'yan Afirka da ke kasashen waje suka amsa kira suka fara shigowa Ghana.
Gabanin wannan shirin, akwai kimanin bakaken fata daga kasashe daban-daban da suka yi kaura zuwa Ghana kimanin dubu 3000, kuma mafi yawanci, batun kwanciyar hankali da walwala ya sa suka zabi zuwa kasar Ghana.
Ghana ta kasance kasa da yawancin Amurkawa bakaken fata, a cikin 'yan shekarun da suka gabata suke yawan ziyarta; wasu ma sun dawo da zamansu na din-din-din a kasar.
Ga wasu, Ghana kasa ce da ba ta da matsala ta tsaro da nuna banbanci. Ga wasu kuma, kasar na baiwa ‘yan kasashen waje damar bunkasa cikin sauki, yayin da suke sajewa da tushensu da al’adun kakanninsu.
Irbard Ibrahim, masanin tsaro da huldar kasa da kasa, ya yi wa Muryar Amurka bayanin yadda wannan shirin ya taimaka wajen shigowar baki Ghana da kuma kara fadada shirin zuwa "Beyond the Return" wato “bayan dawowa”. Yace, dakile matsalar tsaro da kuma tsarin tallafawa baki da ma’aikatar yawon bude ido na daga cikin abinda ya sa Amurkawa bakaken fata suke dawowa Ghana da zama.
A bayaninta, Vanessah Mixon Alawiyi, wata bakar fata ‘yar Amurka, wacce ta ke auren dan kasar Ghana da suka hadu a Amurka, ta bayyana cewa, ta fara zuwa Ghana a shekarar 1990.
Ta ce "Na zo Ghana a 1990 don kasancewa tare da dangi ba a matsayin mai yawon bude ido ba, kuma da na zo sai na saje da jama’a baki daya. Kuma na gaji tunanin zuwa Africa ne daga ‘ya ta da ta rasu. Burinta ne ta dawo Afirka da zama lokacin da take budurwa. Ina farin cikin zama a Ghana. Sai in ce ‘e’, domin babban farin ciki na, a Ghana na samu. Kuma akwai zaman lafiya da tsaro domin zan iya fita da asuba in yi atisaye ba da fargaba ba. Wasu suna zuwa Ghana su yi shekaru hudu su tafi, wasu kuma watanni; domin haka, kowa na da dalilinsa na zuwa Ghana. Ina son abincin Ghana, musamman Hausa jolof, wato dafa dukan hausawa."
Masanin tattalin arziki, Imrana Hashiru Dikeni a nasa bangaren yace, Ghana za ta amfana kwarai da shigowarsu domin za su zo da hannun jari ne da zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar.
Domin karawa masu kaura zuwa kasar kwarin gwuiwa, gwamnatin Ghana ta shirya da Sarakunan gargajiya su ware fili, kadada 500 domin baiwa sabbin masu kaura da za su shigo kasar.
Saurari rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti: