Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce lokacin da mayakan Boko Haram suka shiga garin Baga da misaln karfe 7:15 na dare, ta tura wani jirginta na leken Asiri wato ISR da ma karin wasu jiragen yaki.
Jiragen yakin sunyi ta auna 'yan Boko Haram din inda suka karkashe duk wadanda suka auna din.
Rundunar sojojin saman Najeriyar kamar yadda kakakinta, Air Commoder Ibikunle Daramola ke bayyanawa, sun marawa dakarun sojojin kasa da na Ruwa a doron Baga, yayin da mayakan na Boko Haram suka kai wani farmaki inda aka tura jiragen yaki har shida.
A kudancin garin Baga, dakarun sun hangi jerin gwanon motocin mayakan na Boko Haram, dauke da manyan makamai inda sojojin suka konesu kurmus.
Sojojin saman sun dauki kwamandojin dakarun kasa da na ruwa inda aka kai farmakin dasu tare, a wani kokarin kambaba sha'anin aiki tare.
Rundunar sojin saman Najeriyar tace ta tayar da jiragen yakinta sau 21 kana ta kai farmaki sau 20 cikin awowi 39.
Masanin tsaro Wing Commander Musa Isa Salman, yace duk da wannan Gwamnati tayi rawar gani, wajen marawa dakarun na sama, amma har yanzu akwai bukatar kara masu kayan aiki.
Facebook Forum