Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tsaro Ta Addabi Yankin Tingno a Jihar Adamawa


Yayin da hankulan ke kwantawa a yankin Tingno dake da albarkatun noma, biyo bayan tashin hankali da ya auku a makon jiya inda aka rasa rayuka da dama, yanzu wata matsalar da ke tasowa ita ce batun satar amfanin gona, harin sari ka noke da kuma cunen da mazauna garin ke zargi ana yi.

Wannan na zuwa ne yayin da aka soma sallamar wasu dake kwance a asibiti, sakamakon harbin bindiga ko kuma sara da aka yi musu a rikicin.

Mallam Hussaini yana da cikin wadanda aka harba a hannu da yanzu haka ke kwance a asibiti, inda ya ce, yana samun sauki, kuma ya yazuwa yanzu an salami wasu daga cikin su.

To sai dai rahotanni na cewa har yanzu akan bi wasu a gonaki ana yi musu kisan dauki daidai, tare da sace amfanin gona musamman shinkafa.

Alh.Garba Dauda, wani shugaban al’umma a yankin ya bayyana ya ce, baya ga asarar rayuka da dukiyar da aka yi a farkon tashin hankalin, yanzu haka ana sace musu shinkafa a gonaki. Akan haka suke kira ga gwamnatin tarayya da ta shigo tare da kafa barikin sojoji a yankin domin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawan DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce, jami’an tsaro na iya kokarinsu, inda suka kama fiye da mutum talatin a baya, sannan akwai Karin matakan da aka dauka.

To amma ya musanta zargin nuna bangaranci ko kama wadanda basu ji ba, basu kuma gani ba.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG