A wani sabon yunkurin shawo kan sabbin hare-haren ‘yan bindiga dadi a jihar Zamfara, shelkwatar tsaron Najeriya ta sake kaddamar da wani sabon farmaki mai take “Operation Accord” da ke karkashin “Operation Hadarin Daji”.
Rundunar tsaron kasar ta ce, ta kai sabon farmakin da jiragen yaki a kan sansanonin ‘yan ta'adda a dazukan Tsibiri da Manya da ke karamar hukumar Zurmi, wanda suka sami nasarar hallaka ‘yan bindiga da dama.
Navy Kwamanda Abdulsalam Sani na shelkawatar tsaron Najeriya ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa, rundunar tsaron Najeriya ta samu nasarar kai harin ta sama a sansanonin ‘yan ta’addan da ke dazukan Tsibiri da Manya kuma ta hallaka 'yan bindiga da dama.
Ibrahim Ahmad Janyau, jagoran wata kungiyar da ke fafutukar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara, ya ce, a yanzu suna da tabbacin irin hobbasa da jiragen yakin sojojin Najeriya ke yi a jihar.
Ya kuma yi fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu, duba da yadda shelkwatar tsaron kasar ta sha alwashin kawo karshen ‘yan bindigar.
Ya ce, yanzu abin da suke jira shi ne, ko wannan sabon yunkurin na rundunar sojojin Najeriya zai kai ga samar da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum