Sojojin na musamman karkashin rundunar mayakan saman Najeriya da ke fafatawa a jihar Zamfara biyo bayan rahotannin sirri da suka samu, sun ragargaji wasu gungun 'yan bindiga.
'Yan bindigar da ke cikin Dajin Sabubu da Kagara sun yi yunkurin far ma kauyuka biyu a karamar hukumar Gusau ne, lokacin da sojojin suka taka masu burki, al'amarin da ya janyo musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Daga bisani, sojojin saman sun sami nasara akan 'yan bindigar wadanda suka yi kokarin arcewa kuma dakarun suka bisu har cikin dajin take kuma suka kashe guda biyar tare da raunata wasu da dama, kana aka kwato manyan bindihogi guda uku makare da harsashai.
Harin dakarun na Najeriya, na zuwa ne, kwana guda bayan wani harin 'yan bindiga da ya halaka mutane da dama. Wasu majiyoyi sun ce ana kashe akalla mutum sama da 40, yayin da hukumomin jihar ke musanta wannan ikrari.
Bugu da kari, sojojin saman sun kubutar da mutanen da 'yan bindigar suka sace ciki har da mata biyu da dan jariri.
Kawo lokacin hada wannan rahoto, jiragen yakin sojin saman na can na ta ruwan wuta a Dajin na Sabubu don gamawa da duk 'yan bindigar da ke boye a cikinsa.
Tuni dai Babban Hafsan Rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya nuna gamsuwa da Wamban hobbasa, inda ta tabbatar da za su ci gaba da kare rayukan Jama'a.
A cewar wani masanin tsaro, Kabiru Adamu, in ana son a kawo karshen wannan rikici na jihar Zamfara, ya zama wajibi dakarun su mamaye baki dayan dazukan yankin.