Dakarun na rundunar kawancen kasashen yankin Tafkin Chadin, sunyi wani fafatawa ne mai zafi a yankin kan iyakar Najeriya da Chadi.
Fafatawar da Runduna ta biyu a bangaren Chadi da Runduna ta uku a bangaren Najeriya suka kaddamar na farautar neman yan ta'addan mai take “Operation Yancin Tafki” Ya yi sanadiyyar halaka mayakan Boko Haram 39 a kauyen Cross Kauwa dake dabda tafkin Chadi.
Wata sanarwa da sojojin suka aikewa Muryar Amurka, mai dauke da da hanun Kanar Ezindu Idima, ta ce a bangaren su, sojoji 20 sun Sami raunuka.
Dakarun Hadin gwiwar kazalika sun kuma sun kwato motocin yaki biyu da wasu manyan bindigogi na harbo jiragen sama da kuma karin wasu bindigogi masu sarrafa kansu da harsasai masu yawan gaske.
Tuni dai babban Hafsan Hafsoshin Rundunar tsaro na Chadi Janaral Tahir Erda da Babban Hafsan sojin kasa na kasar suka tsallako kan iyakar Najeriya, inda suka je har Kinnasara a bangaren Monguno don jinjinawa dakarun.
Janar Also Erda ya kuma nemi dakarun da su gaggauta kawo karshen ta'addancin na Boko Haram Akan lokaci.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum