Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DA DANGARI: Tarihin Garin Adarawa a Jihar Maradin Nijar, Janairu 21, 2023


Bandiagara, Mali
Bandiagara, Mali

Shirin Da Dangari na wannna makon ya kai ziyara garin Adarawa a jihar Maradin Jamhuriyar Nijar. A hirarsa da wakilin Muryar Amurka Mansur Sani, Magajin garin malam Sha’aibu Iro, ya ce garin ya kai kimanin shekara sama da 100 da kafuwa.

Garin Adarawa na da yawan al’uma kimanin dubu hudu, da suka hada da kabilar buzaye da gobirawa a cewa malam Iro. Ya kuma ce makiyaya daga Adar da ke yankin jihar Tahoua ne suka kafa garin.

Noma ce babbar sana’ar jama’ar garin sai kuma kiwo. Sai dai Magajin garin ya ce babban kalubalen da manoma ke fuskanta shi ne yadda aka maida gonaki gidaje. Bayan haka malam Iro ya koka game da matsalar ruwa da wadatattun makarantu da ake fuskanta a garin.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

DA DANGARI: Tarihin Garin Adarawa A Jihar Maradin Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:11 0:00

XS
SM
MD
LG