Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Da Da Uba Sun Mamaye Filin Gwamnati a Oregon Ta Amurka


Masu Zanga-Zanga a Jihar Oregon
Masu Zanga-Zanga a Jihar Oregon

Wasu mutane dauke da makami sun mamaye wani ginin gwamnatin tarayya a Arewa maso Yammacin jihar Oregon da ke nan Amurka, bisa jagorancin wasu Uba mai shekaru 73 da dansa dan shekaru 46.

Dama an taba daure uba da dan bisa zargin cinnawa wani dajin gwamnati wuta shekaru da dama da suka wuce, wanda tuni ma suka yi zaman kaso sakamakon wannan laifi na mamaye gandun dajin Malheur.

Kwanan nan dama wani alkali ya soke wa’adin da suka yi a gidan maza. Inda yayi umarnin da uba da dan su sake dawowa don kara yin wasu shekarun a gidan wakafi.

A cikin shugabannin dogarawan filin har da ‘ya’yan wani mai gidan gonan nan na Nevada Cliven Bundy har su 3, wanda ya taba jagorantar yin carko-carko a wani wajen da ke karkashin ikon gwamnatin tarayya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG