A jamhuriyar Nijar matan dake kwance a Asibiti masu fama da cutar yoyon fitsari, sun bukaci jama’ar cikin gida da waje su agaza da kayan kula da tsaftar jiki da dai sauran abubuwa na bukatun yau da kullum, musamman a wannan lokaci na shiga yanayin zafi.
Kiran dai tuni ya samu karbuwa daga wata kungiyar inganta rayuwar mata da yara da ake kira CODECO.
Daruruwan mata ne galibinsu matasa ke kwance a asibitin kula da masu fama da yoyon fitsari, wadda hukumomin Nijar suka kafa a shekarun baya a birnin Yamai, da zummar ceto rayuwar wadanda suka tsinci kansu cikin wannan mugun alkaba’i.
Saboda haka kungiyar CODECO mai zaman kanta ta ziyarci wadanan matan, don jin irin matsalolin dake damunsu a wannan lokaci na shigar zafi, Mariama Issa ita ce jagorar wannan kungiya. Cikin yanayin murna da farin ciki wadanan matan suka yiwa tawagar masu bada tallafi bayanin abubuwan da suke bukata.
Kungiyar ta CODECO wace ke kula da matsalolin mata da matasa ta yi alkwalin shafe hawayen wadanan matan da matsalar yoyon fitsari ta raba su da dangi su, saboda kyama ko kuma dalilai masu nasaba da talauci.
Matsalar yoyon fitsari na kan gaba a jerin matsalolin da gwamnatin Nijar ke fadi tashin ganin an murkusheta, cikin hanzari sai dai da alama wannan yaki na bukatar gudunmawar kowa da kowa inji Hachimou Hajia Zara shugabar asibitin mata masu cutar yoyon fitsari.
Likitoci sun sanar da cewa aurar da ‘yan matan da ba su kosa ba, da rashin zuwa awon ciki na daga cikin matsalolin da ke haddasa kamuwa da cutar yoyon fitsari.
Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Facebook Forum